Hukumar tace finafinai da ɗab'i ta jihar Kano ta bayyana shirinta na fara shirya fim ɗin kurame a jihar.
Abba El-Mustapha, shugaban hukumar, shi ne ya bayyana hakan lokacin da ƙungiyar kurame ta kai masa ziyara a ofishinsa.
El-mustapha "ya yi wa mambobin ƙungiyar alƙawarin haɗa su da dukkan wani da ake tunanin zai iya taimaka musu a ciki da wajen masana'antar Kannywood," a cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar.
Da yake magana yayin ganawarsu, jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar Kurame Rabi'u Aliyu Adam ya ce suna da gudummawar da za su iya bai wa al'umma musamman masu buƙata ta musamman.
"Manufar fara shirya finafinan ita ce samar da aiki ga kurame baya ga ilimantarwa tare da nishaɗantar da sauran masu buƙata ta musamman," in ji shi.
Rabi'u ya faɗa wa El-Mustapha da cewa tuni suka fara shirya wasu finafinai na kurame ta hanyar amfani da wayar salula, kamar yadda sanarwar ta bayyana, kuma ya nemi taimakon gwamnatin Kano wajen cikar burinsu.