An yi Walimar Buɗe Wani Sabon Gidan Biredin Annour Bakery A Azare 

Hussain Muhammad Danliti


A ranar Talata a gabatar da buɗe wani sabon gidan Biredin Annour Bakery da


Alhaji Abubakar Abdulkadir Shekarau (Ɗan Iyan Azare) kuma (Dagacin Kafin Tatari Ali Azare) ya bayyana cewa wannan aikin alheri rage yawan masu zaman banza a cikin al'umma aikin alheri ne ya yabawa shugaban sabon gidan Biredi, ya mai cewa duk lokacin da wani ya buɗe wata ma'aikata baya buɗewa kansa bane ya buɗewa al'umma baki ɗaya tare da ƙaramar hukumarsa, jiharsa da kuma ƙasarsa baki ɗaya. 

Ya ƙara da cewa domin ya rage masu zaman banza marasa aikin yi. yayi kira ga masu neman aikin a ma'aikatan gidan sabon Biredi da su rike amana da gaskiya idan sunyi nasarar samu aikin a ma'aikatan domin inganta aikinsu da rayuwarsu. Ba yadda za a yi mutum ya dauka ka kayi masa aiki, amma rashin gaskiya da cin amana ko hassada da muguta ta shiga ranka. 


Shugaban majalisar malamai na Katagum reshe kungiyar Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa'ikamatul Sunnah (JIBWS), Mallam Magaji Baffah Suleiman yayi jawabi nasiha da wa'azi domin tunatar da al'ummar, ya kawo da misalin Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wa Sallama), ya ce Mafi alheri mutane shi ne mutumin da yake amfanar al'umma. (Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallama.) ya ce akwai alheri tattare da wannan mutumin. 

Malamin ya ƙara da cewa allar hakiƙa alkalama tattalin arziki suke ambatawa cewa da ce kungiyoyin da kamfanoni za a buɗen kamfanoni a sassan ƙasar da idan mutum ya kammala karatunsa ba zai jira dole sai aikin gwamnati, zai nemi aikin kamfani domin inganta rayuwarsa.


Yana mai cewa yanzu masu hannu da shuni sai dai sukai kuɗaɗensu banki ko su saya wasu kadarori na filaye, gidaje, basa amfana da kuɗaɗensu wajen amfanar da al'umma. Sai kaga muum ya mallaki wasu kuɗaɗe masu tarin yawa, amma rashin sa'a al'umma basa amfana da wannan kuɗaɗen nasa. Ya ce irin waɗannan mutum basu taimakawa tattalin arziki ba, basu taimakawa al'umma ba. 

Alarammah Ahmad Aliyu ya karanta wasu ayoyi guda uku daga Alqur'ani mai girma tare da addu'ar Allah Ta'ala ya sanya alheri a sabon gidan Biredi yasa ya amfani al'ummar Katagum baki ɗaya. 


Alhaji Falalu Attah (Galadiman Ragwa) ya bayyana cewa zai yi magana game da batun biyu na ɗaya rike amana da gaskiya, na biyu dukkan manyan Katagum ya kamata su kawo wani ingantaccen cigaba wa ƙasa kuma haifarsu Katagum.


Na farko shi ne  ma'aikatan da aka dauka aiki a sabon gidan Biredi su zamo masu rike amana da gaskiya, rashin rike amana da gaskiya shi kake kawowa rashin ingantaccen ci gaba a cikin al'umma. 

Ya ƙara da cewa na biyu kuma shi ne manyan mahukunta, jami'an tsaron, sarakunan gargajiya, 'yan siyasa da 'yan kasuwa suyi iya baki kokarin wajen ganin sun kawo ingantaccen ci gaba wa ƙasar Katagum ɗin don rage yawan masu zaman banza a cikin al'ummar ƙasar. 

Ya ƙara bayyana cewa akwai manyan mahukunta ƙasar Katagum masu arziki wadda ya kamata ace sun kawo ingantaccen ci gaba wa ƙasar, amma har yanzu sun gagara yin hakan. 

Don haka ina ƙara kira garesu da su taimaka wajen kawo ci gaba wa al'ummarsu, sun yi kokarin kawo kamfanonin don inganta rayuwar matasan Katagum, idan an kafa kamfanonin a garin za a ƙara samu ingantaccen ci gaba daga ko ina za a iya zuwa a saya kaya a Katagum. 

Ba tsammanin wani/wata wadda zai zo daga wani waje ya ce zai kafa kamfanonin a Katagum dole sai dai ɗan ƙasar kuma haifaffen wajen shi zai iya kawowa ingantaccen ci gaba a Katagum ɗin. Ya ƙara da cewa don haka muna kira zuwa ga masu hannu da shuni su zo su kafa kamfanonin a Katagum don ƙara inganta mahaifarsu. 

Karamar Hukumar Katagum suna da marasa ayyukan yi da yawa a cikinsu akwai masu karatun Digiri, Diploma, NCE, waɗ'anda suka kammala karatunsu, amma babu ayyukan yi a ƙasa.

Ya ƙara da cewa an yanzu idan na neman masu karatun Digiri, NCE, zaka samu guda 5000 don haka muna ƙara kira zuwa ga masu hannu da shuni da suka kamfanonin a ƙaramar hukumar Katagum domin inganta rayuwar al'umma.  

أحدث أقدم