Gidauniyar Gadi-Care Za Ta Dauki Dawainiyar Karatun Dalibai 200 A Katagum 

Gidauniyar Gadi-Care za ta dauki dawainiyar mayar da dalibai 200 da suka bar makaranta saboda matsin rayuwa a yankin karamar hukumar Katagum dake jihar Bauchi. 

Gadi-Care gidauniya ce ta sa-kai wadda ke taimakawa marasa galihu musamman a fannin ilimi da dogaro da kai. 

A cikin wata sanarwa da sakataren Gidauniyar Kabir Nizam Baba, Esq, AICMC ya fitar a shafinsa na sada zumunta ya ce “Gidauniyar ta shirya shigar da yara dari biyu (200) makaranta da daukan dawainiyarsu a wannan shekara tare da gabatar da lakca akan maudu'in 'Muhimmancin ilimi ga cigaban alumma' wadda Farfesa Yakubu Magaji Azare zai gabatar insha Allahu”.

Ya kara da cewa “Bugu da kari, za a gabatar da lambobin yabo (awards) don karramawa ga wasu daga cikin mutane da suke bada taimako wajen tallafawa ilimi da hidimtawa al'umma”.

“Za ayi wannan taro qarfe 9:30am na ranar Lahadi, 1 ga watan Junairun 2023 insha Allahu a dakin taron Sakateriyar COEASU da ke Kwalejin ilimi ta Aminu Saleh da ke Azare” Inji shi. 

Daga karshe ya gayyaci dukkan al'ummar karamar hukumar Katagum domin halartar wannan taro tare da fatan sanya su cikin addu'ar Allah idda nufi, Ya kuma sa ayi lafiya. 

أحدث أقدم