Takaitaccen Tarihin Mallam Babba Na Kofar Gabas

Mallam Babba na kofar gabas shahararren malamin addinin musulunci ne wanda ke zaune da Almajiransa a unguwar Kofar Gabas a cikin garin Azare dake karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi. 

A wata ziyara da wakilin KATAGUM DAILYPOST ya kai wa Mallam Muhammadu Babba watau dan mallam Babba wanda ya gaje shi wajen bada karatu, ya shaida masa cewa Mallam Babba ya rasu a shekarar 2008 a gidansa da ke Ƙofar Gabas, ya rasu yana da shekaru sama da casa'in a duniya.

Kakan Mallam Babba wato Malam Mai Gezo mazaunin Masanawa ne dake Æ™asar Katsina ne, inda su ka yo Æ™aura zuwa Katagum Mai Kaba, wato helkwatar karamar hukumar Zaki, wanda a nan garin ne (Katagum Mai Kaba) aka haifi Mallam Babba. Inda daga bisani kuma suka sake yin  Æ™aura zuwa cikin garin Azare.

Sai dai wasu sun ce kakan Malam Babba ba wai Æ™aura Yayo Ba, sai dai zamu iya cewa ana kiransu da Muhajirun watau su matafiyane daga birnin Katsina zuwa Saudiyya, sun yi zango a Kano inda sarkin Kano na wancan lokacin yayi-yayi su zauna da shi amma sun Æ™i, suka ce sun fito ne domin tafiya Saudiyya ne amma da zuwan su Katagum domin su ya da zango saboda yadda su ka ga an karbesu sai suka ce nan Allah ya yi zamansu amma sun bar 'É—ayan su a Kano É—aya kuma a Hadejia, dama su uku suka shigo Katagum,  kuma cikin ukun akwai Wakilin katagum Wakili Babban Yaya, wanda aka nada shi a shekarar 1904. 

Bayan rasuwar sa an naÉ—a É—ansa Wakili Hassan,  bayan rasuwar Wakili Hassan, É—an sa Muhammad Bawaji Hassan bai nemi sarautar ba,  sauran ma basu nema ba sai tsohon gwamnan Bauchi Abubakar Tatari Ali ya nema wa wansa, kuma har yanzu su ne suke yin wannan sarautar.

Allah Ya albarkaci Mallam Babba da ƴaƴa mata guda huɗu da maza biyu. Matan Mallam Babba su biyu ne, su ma Allah ya karɓi ransu.

Allah ya gafarta wa Mallam Babba na Ƙofar Gabas da iyalansa baki daya!

Waɗanne baitika za ku iya tunowa a waƙar da Marigayi Alh. Mamman Shata Katsina ya rera mai taken "Mallam Babba Na Ƙofar Gabaa?"
Previous Post Next Post